
Rahotanni daga fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na cewa, an garzaya da jirgin shugaban kasar zuwa kasar Afrika ta kudu dan yi mada fenti da sauran Gyare-Gyare.
Wata majiya daga fadar shugaban kasar ce ta bayyanawa kafar Jaridar Punchng haka inda tace za’awa jirgin Fenti ne irin na tutar Najeriya da sauran ‘yan Gyare-Gyaren.
Rahoton yace zuwa yanzu, an kashe Naira Biliyan N20.03bn waja kula da jiragen shugaban kasar cikin abinda bai wuce shekara guda ba.
Jiragen shugaban kasar Najeriya na daya daga cikin manya a Nahiyar Afrika.