Friday, December 5
Shadow

An gurfanar da matashin da ya hau kan allon talla saboda dan Tiktok a kotu

An gurfanar da matashin da ya hau kan allon talla saboda dan Tiktok a kotu.

Rundunar ‘Yansandan Jihar Kano ta gurfanar da wani matashi mai shekaru 19 mai suna Ibrahim Abubakar, bisa laifin yunkurin kashe kansa, bayan da ya hau wata babban karfen talla a Kano ya kuma yi barazanar yin tsalle daga sama, yana danganta hakan da rashin ganin fitattun taurarin TikTok da yake kauna.

Abubakar, dan asalin jihar Adamawa, ya tayar da hankula a ranar Litinin a Gadar Lado da ke kan titin Zariya, lokacin da ya hau saman wani Babban allon talla ya kuma yi ikirarin zai kashe kansa idan har fitattun masu TikTok da yake bibiyarsu ba su bayyana a wurin ba.

Karanta Wannan  TIRKASHI KALLI BIDIYO: Yan Kaduna Sun Yiwa Bilal Villah Ruwan Duwatsu, Lokacin da yaje gabatar da wasan sallah

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma’a, Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yansanda a jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da cewa an gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotun Majistare mai lamba 5 da ke Gyadi-Gyadi, Kano, bisa zargin yunkurin kashe kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *