Garin Bacup dake karkashin Lancs a kasar Ingila ya hana wani kamfanin yin Pizza, me suna Woody’s Pizza ya bude reshe saboda a cewar mahukuntan garin yaran garin kib ta musu yawa.
Woody’s Pizza sun so bude reshene a wani tsohon shagon barasa da aka kulle kuma sun ce suna aka sukari da gishiri kadan a Pizza dinsu sannan zasu rika sayen kayan yin Pizza din daga kasuwar garin.
Saidai mahukuntan garin sun ce basu yadda ba.
Ko da a shekarar 2023 ma, mahukuntan garin Bacup sun taba hana bude wajan cin abinci saboda irin wannan dalili.