Tuesday, April 29
Shadow

An hana bude wajan Sayarda Pizza a kasar Ingila saboda tana sa yara kibar data wuce kima

Garin Bacup dake karkashin Lancs a kasar Ingila ya hana wani kamfanin yin Pizza, me suna Woody’s Pizza ya bude reshe saboda a cewar mahukuntan garin yaran garin kib ta musu yawa.

Woody’s Pizza sun so bude reshene a wani tsohon shagon barasa da aka kulle kuma sun ce suna aka sukari da gishiri kadan a Pizza dinsu sannan zasu rika sayen kayan yin Pizza din daga kasuwar garin.

Saidai mahukuntan garin sun ce basu yadda ba.

Ko da a shekarar 2023 ma, mahukuntan garin Bacup sun taba hana bude wajan cin abinci saboda irin wannan dalili.

Karanta Wannan  A karshe dai bayan shan ruwan Allah wadai, Gwamnatin tarayya na shirin yafewa kananan yaran data kai kotu bosa zargin cin amanar kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *