
Wannan wani fasto ne dan kimanin shekaru 35 me suna Goitsekgosi Mojadigo da kasar Botswana wanda aka yankewa hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari
An yanke masa hukuncin ne bayan samunsa da laifin yiwa wata matashiya me shekaru 23 fyade.
Matashiyar dai ta he wajansa ne neman ya mata addu’ar samun aiki inda shi kuma yace sai an tsarkake ta tukuna.
An kuma zargi Faston da zakewa mata masu kananan shekaru da dama a cocin nasa.