
‘Yansanda a jihar Edo sun kama wani magidanci me sunan Kelvin Izekor bisa zargin kashe matarsa.
Makwabtansu sun bayyana cewa, Kelvin da matarsa, Success Izekor basu dade da yin aure.
Bidiyon lamarin da ya faru ya karade shafukan sada zumunta inda aka ga ‘yansanda sun dauke gawar matar da sarar adda akanta.
Kakakin ‘yansandan jihar, Moses Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace mafusatan matasa sun so kashe mijin amma zuwan ‘yansanda suka yi nasarar kubutar dashi.
Yace sun tafi da mijin dan gudanar da bincike inda yace sun kai matar Asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ta mutu.
Yace duk wanda aka samu da laifi za’a hukuntashi.