Tuesday, May 19
Shadow

An kama magidanci da ya Kkàshè matarsa

‘Yansanda a jihar Edo sun kama wani magidanci me sunan Kelvin Izekor bisa zargin kashe matarsa.

Makwabtansu sun bayyana cewa, Kelvin da matarsa, Success Izekor basu dade da yin aure.

Bidiyon lamarin da ya faru ya karade shafukan sada zumunta inda aka ga ‘yansanda sun dauke gawar matar da sarar adda akanta.

Kakakin ‘yansandan jihar, Moses Yamu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace mafusatan matasa sun so kashe mijin amma zuwan ‘yansanda suka yi nasarar kubutar dashi.

Yace sun tafi da mijin dan gudanar da bincike inda yace sun kai matar Asibiti inda likita ya tabbatar da cewa ta mutu.

Yace duk wanda aka samu da laifi za’a hukuntashi.

Karanta Wannan  An dakatar da dan Bautar Kasa bayan da ya bayyana cewa Zai Aikata Alfasha da dalibai mata saboda ya gansu da Manyan Nòwnùwà da Manyan Màzàunàì a Jihar Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *