
Kotu a jihar Bauchi na shirin yanke hukunci kan wani malamin jami’a da ya wallafa tsohon Bidiyon dan gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad yana rawa.
A yau Alhamis ne ake sa ran kotun zata yanke hukuncin neman belin malamin me suna Dr. Abubakar Ahmad wanda dan gwamnan me suna Shamsudeen Bala Mohammed ne ake zargin ya shigar dashi kara.
Malamin na koyarwa ne a kwalejin Federal College of Horticulture dake jihar.
An kamashi ne saboda wani tsohon Bidiyon da ya wallafa na dan Gwamnan da matarsa suna rawa.
Me ikirarin kare hakkin bil’adama kuma mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore ne ya wallafa hakan.
Yace An tsare malamin makarantar na tsawon makonni 2 bisa cin zarafi da rashin adalci.
Matar malamin me suna Fatima ta nemi a saki mijinta.
Fatima ta yi kira ga Gwamna Bala da ya saka baki a lamarin dan jawo hankalin dansa ya janye karar da ya shigar akan mijinta dan suna cikin wani hali.
Lauyan Malamin, Ahmed Hassan, Esq. Ya bayyana cewa, a doka wannan laifin bai kai a tsare mutum ba amma ‘yansanda sun tsare malamin, yace kuma ko da za’a tsare malamin bai kamata ya wuce awanni 24 ba.
Ya bayyana cewa a ranar 11 ga watan yuni ne dai ‘yansanda suka gayyaci wanda yake karewa zuwa ofishinsu inda kuma shi baya gari kuma ya bashi shawarar ya je ya amsa gayyatar da aka masa.
Yace amma yana zuwa sai aka tsareshi, yace suna ta neman a bayar da bilinsa amma abu ya faskara.