Friday, July 17
Shadow

Da Duminsa: Hukumar ‘yansandan farin kaya ta kama masu satar mutane dan neman kudin fansa su 6 a filin jirgin sama dake Kaduna bayan da suka dawo daga aikin Hajji

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, hukumar ‘Yansandan farin kaya DSS ta kama masu garkuwa da mutane 6 da suka dawo daga aikin Hajji a filin sauka da tashin jiragen saman jihar.

An kamasu ne da misalin karfe 3:40am kamar yanda wata majiya ta gayawa majiyarmu.

Wadanda aka kama din mata 3 ne maza 3 kamar yanda rahoton ya tabbatar.

An kama su ne da daren ranar Talata.

Zuwa yanzu dai ba’a fitar da bayanai kan sunaye ko hotunan wadanda aka kama din ba.

Ko da a watan Mayu da ya gabata dai an kama wani me garkuwa da mutane me suna Sani Galadi da ke shirin tafiya zuwa aikin Hajji.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Tun ina Yarinya 'yar Shekara 5 na gano karyar da ake mana a coci, daga nan na ji soyayyar Annabi Muhammad(Sallalahu Alaihi Wasallam) ta shiga Raina kuma na zabeshi a matsayin Masoyi, Munirat Abdulsalam ta gayawa Kiristoci masu ce mata ta koma Kirista

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *