Wednesday, January 1
Shadow

An kama matar da ake zargi da kai wa Bello Turji makamai daji a Zamfara

Bataliyar rundunar sojin Najeriya mai yaƙi da yan fashin daji a arewa maso yammacin Najeriya da ake kira da Operation Fansar Yamma, ta samu nasarar cafke wata mata mai shekaru 25 da haihuwa dauke da alburusai 764 da kuma bindigogi guda shida, da ake zargin za ta kai sansanin madugun ƴan fashin dajin nan Bello urji

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar laftanal kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce an kama matar ne a ranar 28 ga watan Disamban 2024 da ake ciki, tare da wani abokin tafiyarta a yankin Badarawa da ke karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.

Kamen dai ya biyo bayan wani rahoton sirri da aka samu game da safarar makaman ƴan bindigar a kan hanyar Kware zuwa Badarawa a karamar hukumar ta Shinkafi.

Karanta Wannan  Sace karafan titin jirgin kasa ya haddasa hadarin jirgin kasan dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja

Bayan samun waɗannan bayanai ne dakarun rundunar ta Operation Fansar Yamma suka kafa wani shingen bincike wanda ya kai ga cafke wadanda ake zargin.

A halin yanzu dai ana ci gaba da bincikar mutanen da aka kama.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar ta ƙuduri aniyar ci gaba da daukar dukkan matakan da suka kamata domin daƙile safarar makamai ga ƴan bindigar, da ke ci gaba da tayar da zaune tsaye a yankin.

Don haka ta yi kira ga jama’a da kada su gajiya wajen bayar da sahihan bayanan da za su kai ga samun wannan nasara, da ma kamo su kansu ƴan bindigar da aka jima ana nema ruwa a jallo.

Karanta Wannan  Kimanin Mabiya Shi'a Guda Dari Ne Suke Tsare A Hannun Jami'an 'Yan Sandan Abuja Bisa Zargin Su Da Kashe Jami'an Tsaro A Yayin Tattakin Arba'in Da Suka Gudanar A Abuja A Makon Da Ya Gabata

Dama dai an jima ana zargin akwai masu kai wa ƴan bindigar makaman da suke amfani da su har dazukan da suke a wannan yanki musamman ita Zamfara, da ta fi fama da wannan matsala.

Ko a watan Nuwamban da ya gabata ma sai da rundunar ƴan Sandan Jihar ta kama wani ɗan ƙasar Aljeriya, mai shekaru 58 kan zargin safarar makamai daga wasu ƙasashe maƙwabtan Najeriya inda ya ke shiga da su ta Zamfara.

A wannan lokaci kwamishinan ƴan sandan jihar Mohammed Dalijan, ya faɗawa BBC Hausa cewa sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 16, yayin samame daban-daban da suka kai cikin makonni uku da suka gabata sakamakon bayanan sirrin da suka samu daga shi wannan mutumi.

Karanta Wannan  'Yan ta'adda sun kwace iko da sansanin horas da soji mafi girma a Najeriya

Kana ya bayar da bayanan wasu mutanen suma da suke samar da makaman a Jos, jihar Plateau, da suma ake safararsu zuwa yanki.

Hakazalika, sun samu wasu manyann bindigogi guda biyu da wata bindiga ƙirar gida daga hannun wani mai ƙera makamai a Jos, Jihar Filato.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *