
Mahukunta a jihar Legas sun kama wani mutum me suna Gbolahan Adebayo bida zargin kashe budurwarsa.
Adebayo dan shekaru 23 ya daki budurwarsa me shekaru 25 har ta mutu.
Lamarin ya farune a ranar 21 February 2025 kamar yanda Daily Post ta ruwaito.
Kakakin ‘yansandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace abin ya farune a Ijedodo, Isheri-Osun dake jihar.
Wani makwabci daya shaida lamarin yace ya ji Adebayo na dukan budurwar tasa kuma da aka leka aka tarar bata motsi, saidai zuwa yanzu ba’a san dalilin da yasa ya kashe budurwar tasa ba.
Tuni dai aka kai ta Asibiti inda likitoci suka tabbatar da ta mutu.