Friday, July 17
Shadow

Dalibin jami’a ya nutse ya mutu a ruwa bayan da aka saka masa Naira 300 idan ya tsallake ruwan da iyo

Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin jami’ar Federal University, Otuoke jihar Bayelsa ya nutse a ruwa bayan da suka yi caca shi da abokansa.

Dalibin sun yi gaddama da abokansa kan cewa, ba zai iya tsallake wani ruwa bane da iyo inda shi kuma yace zai iya.

Anan ne sai suka saka Naira Dari uku kowannensu shi da abokansa.

Ya shiga ya fara iyo a cikin ruwan sai suka ga ya nutse, har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba’a gano gawarsa ba.

Rahoton jaridar Punchng ya bayyana cewa an yi kokarin tuntubar hukumar makarantar dan jin ta bakin kakakin makarantar Ms Mercy Ekott, saidai an ta kiran wayarta amma taki dagawa.

Karanta Wannan  Gidana na Alfarma da ake ta cece-kuce akai na ginashi ne tun kamin in zama Minista>>Inji Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu

An kuma tuntubu kakakin ‘yansandan jihar, Mr Musa Mohammed inda yace bai san da maganar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *