
Mun Kama Sojojin Da Aka Tura Maga Amma Suka Bar Wurin Aikin Su Har Aka Sace Dalibai, Cewar Minista Matawalle
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa an kama wasu dakarun soji da aka tura makarantar Maga a Jihar Kebbi domin bayar da tsaro, amma suka bar wurin a ranar da ‘yan bindiga suka sace ɗalibai mata.
Ministan ya ce ana gudanar da bincike don gano ainihin dalilin da ya sa suka bar makarantar a irin wannan lokaci mai haɗari. Ya ƙara da cewa: “Da zarar an kammala bincike, za a ɗauki mataki bisa ka’ida, kamar yadda dokokin soja suka tanada.”
Har yanzu dai ana cigaba da fafutukar ganin an ceto daliban da aka sace.