Tuesday, May 19
Shadow

An kama sojojin da aka aika su tsare makarantar ‘yan mata ta jihar Kebbi amma suna koma daukar hoto da ‘yan matan sannan suka tafi yawo

Mun Kama Sojojin Da Aka Tura Maga Amma Suka Bar Wurin Aikin Su Har Aka Sace Dalibai, Cewar Minista Matawalle

Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa an kama wasu dakarun soji da aka tura makarantar Maga a Jihar Kebbi domin bayar da tsaro, amma suka bar wurin a ranar da ‘yan bindiga suka sace ɗalibai mata.

Ministan ya ce ana gudanar da bincike don gano ainihin dalilin da ya sa suka bar makarantar a irin wannan lokaci mai haɗari. Ya ƙara da cewa: “Da zarar an kammala bincike, za a ɗauki mataki bisa ka’ida, kamar yadda dokokin soja suka tanada.”

Har yanzu dai ana cigaba da fafutukar ganin an ceto daliban da aka sace.

Karanta Wannan  Wannan matar na kira ga Yarbawa da su sheke Hausawa a Legas idan Tinubu bai ci zaben 2027 ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *