Friday, December 5
Shadow

An kashe ƴan China biyu a jihar Abia

Rundunar ƴansandan jihar Abia da ke kudu maso kudancin Najeriya ta tabbatar da kashe wasu ƴan ƙasar China guda biyu da wani ɗansanda mai ba su kariya.

Rundunar ta ce ƴansanda sun ɗauki ne bayan rundunar ta samu kiran kar-ta-kwana cewa wasu gungun mahara sun kai wa ƴan Chinan da ƴansanda da ke rakiya hari a hanyarsu ta zuwa kamfaninsu da ke titin Agukwu-Amaya a garin Ndundu a ƙaramar hukumar Isuikwuato na jihar.

A wata sanarwa da tashar Channels ta ruwaito daga kakakin rundunar ƴansandan jihar, Maureen Chinaka yana cewa an kashe Mista Quan wanda shi ne manajan kamfanin da Mista Cai abokin aikinsa da Insfekta Audu Saidu.

Karanta Wannan  Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar Ya Naɗa Babban Malamin Addinin Musulunci, Farfesa Mansur Sokoto Sarautar Danmasanin Daular Usmaniyya

Rundunar ta ƙara da cewa jami’anta sun samu nasarar ceto wasu ƴan China huɗu da ƴansanda guda biyu.

A sanarwar, kwamishinan yansandan jihar, Danladi Isa ya ce jami’ansa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba har sai sun kama waɗanda suka aikata kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *