
A Najeriya, wasu kamfanonin sufurin hajji da umarah na Najeriya sun bayyana janyewarsu daga hada-hadar aikin hajjin bana, saboda yadda suka ce hukumar alhazan Najeriyar tana gudanar da wasu ayyuka da kamfanonin ya kamata su riƙa aiwatarwa.
Malam Haruna Isma’il shugaban ɗaya daga cikin kamfanonin uku, ya ce sun kwashe tsawon shekara uku suna neman a yi gyara, amma ba a yi komai ba.
Malam Haruna Isma’il shugaban kamfanin harkar sufurin hajji da umarah na Annur Air Services ya karan-tsaye da wuce gona da iri da acewarsa suke cutar da alhazai da masu harkar jigilar ne suka sa suka yanke shawarar janyewa daga aikin.
Mun dai nemi jin ta bakin jami’ar hulɗa da jama’a ta hukumar alhazai ta Najeriya, wadda ta yi alƙawarin aiko mana da nasu martanin kan wannan batu, amma har ya zuwa yanzu babu bayani daga wajenta ba.