Mutane 200 ne aka kashe a sabon harin da aka kai jihar Benue.
Wadanda aka kashe din sun hada da sojoji da ‘yan gudun Hijira da mata da yara.
Lamarik ya farune a kauyukan Yelewata da Daudu dake karamar hukumar Guma a jihar.
Rahoton yace sojoji 5 ne cikin wadanda aka kashe din.
Kamin faruwar harin, an samu bayanan sirri cewa hakan zai iya faruwa.
Matasa da jami’an tsaro sun shirya tare maharan amma sun musu yawa inda suka sha karfinsu suka afkawa ‘yan gudun Hijira.
Mutane da yawa an konasu a gidajensu inda wasu kuma aka konasu a shagunansu dake kasuwa.
‘yansanda dai sun ce suna bin sahun maharan.
Munin hotunan harin yasa ba zamu iya wallafa muku su ba anan.