
Wata malamar coci me suna Annastasia Kinse wadda ‘yar Asalin jihar Filato ce dake a matsayin malamar cocin Katolika dake jihar Edo tace an koreta daga aiki ne saboda ta ki yadda ta zama karuwa a cocin kowa ya rika nemanta.
Ta bayyana hakane a hirar da aka yi da ita a jaridar Punchng.
Kinse itace reverend sister ta farko a kauyensu kuma tana aiki da jami’ar Veritas University sannan tana karatun digiri na biyu, watau Masters a jami’ar Abuja kamin a koreta daga aiki.
Tace a shekarar 2015 ne ta shiga aikin cocin kuma ta y aiki da cocin na tsawon shekarau 2 kamin ta samu kwarewa.
Tace a watan July na shekarar 2025 ne aka fitar da takardar cewa an koreta daga cocin saboda ta koma musulma, amma ace karyane saboda ta kai karar nemanta da lalata da aka yi n yasa aka koreta.
Tace tabbas ta yi rubutu a shafinta na Facebook inda tace ta musulunta amma ba da gaske take ba, tace akwai ‘yar uwarta me suna Salamatu data rasu to ana cikin damuwa ne shiyasa ta rubuta hakan.
Ta kara da cewa, maganar gaskiya, shugabanta a cocin ya nemeta da lalata amma ta ki yadda kuma tana da Bidiyon da sautin murya a matsayin shaida amma aka nemi a mayar da laifin kanta maimakon a hukunta ainahin mai laifin.
Ta bayyana cewa, a karshe korar kare aka mata, aka watsar mata da kaya waje.
Tace amma har yanzu tana neman a mata adalco game da wannan lamari.