
An daure wani direban babbar mota tsawon shekaru 14 saboda ya cire kwandam yayin da yake jima’i da budurwarsa ba tare da ta sani ba.
Wannan mutumi me suna Laurence Rafter, dan kimanin ahekaru 43, ya hadu da wadda yawa wannan laifi me shekaru 32 a wata kafar sadarwa ta yanar gizo ne.
Saidai ya bata sunan karya da Address din karya sannan yace mata yana da katon gidan Alfarma.
Hakanan sun hadu inda suka yi jima’i amma kamin su fara ta gaya masa cewa yasa kwandam, kuma ya yadda ashe suna cikin yi ya cire bata sani ba.
Bayan sun rabu ya ce mata yana dauke da cutar kan jamau amma daga baya aka gane karya yake kawai dan ya bata tsorone, mutumin dake zaune a north London an daureshi shawon shekaru 14 bayan samunsa da laifi.