Saturday, March 15
Shadow

An saci Naira Miliyan 329 daga bankunan Najeriya ta hanyar amfani da BVN na Jabu

Hukumar dake kula da warware sarkakiyar kasuwanci tsakanin bankunan Najeriya NIBSS ta bayyana cewa an yi amfani da BVN na karya aka sace Naira Miliyan 329 daga bankunan Najeriya.

Hukumar tace wasu gungun ‘yan Damfara ne suka rika amfani da hotunan mutane hadda ‘yan kasashen waje suna basu sunayen ‘yan Najeriya suka bude BVN.

Rahotan yace bayan an bude BVN din an yi amfani dashi aka bide accounts a bankuna daban-daban na kasarnan wanda dasu ne aka yi amfani aka yi damfarar.

An dai kulle wasu daga cikin account din da aka yi amfani dasu wajan yin wannan damfarar sannan an kai rahoton wasu masu POS da aka yi amfani dasu wajan damfarar gurin jami’an tsaro.

Karanta Wannan  Ban san an kama kananan yara ba>>Gwamna Abba Kabir Yusuf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *