
An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da fiye da shanu 100 a jerin hare-haren da aka kai kan makiyaya a ƙauyuka biyu da ke cikin Kananan Hukumomin Jos na Kudu da Jos na Arewa na Jihar Filato.
Hare-haren, wanda ake zargin wasu ’yan bindiga ne suka kai ta hanyar buɗe wuta kan makiyayan da ke kiwo, sun sake jaddada yadda tsaro ya taɓarɓare a yankunan da ke fama da rikice-rikicen da ke tsakanin manoma da makiyaya, rikice-rikicen da a kullum ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi.
Sakataren ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya zargi matasa ‘yan kabilar Berom daga ƙauyukan da abin ya shafa da hannu a hare-haren.
Sai dai shugabancin ƙungiyar matasan Berom ya musanta zargin, inda suka bayyana shi a matsayin farfaganda kawai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin farko ya faru ne da yammacin Talata a kauyen Gero da ke Jos na Kudu, yayin da na biyu ya faru da safiyar Laraba a kauyen Darwat da ke cikin ƙaramar hukumar Riyom.
A cewar Babayo, makiyaya uku sun jikkata a harin da aka kai a Gero inda ɗaya daga cikinsu yana karɓar magani a asibiti da ke Jos, yayin da sauran biyun ke jinya a asibitin Sojoji na Rukuba Barracks, Jos.