Tuesday, May 13
Shadow

An shiga rudani a jami’iyyar APC, hankalin kowa ya tashi yayin da ake rade-radin gwamnan Jihar Kebbi zai fice ya koma PDP bayan Atiku Abubakar kamin zaben 2027

Rahotanni daga jam’iyyar APC na cewa jam’iyyar na cikin rudani saboda ana tsammanin gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris na shirin ficewa daga jam’iyyar kamin zaben shekarar 2027 dan komawa PDP bayan Atiku Abubakar.

Hakan ya farune bayan bayyanar wani rahoto da ya ce akwai gwamnonin APC 5 dake shirin ficewa daga jam’iyyar dan komawa PDP kamin zaben 2027 dan su goyi bayan Atiku, kuma sunan Gwamna Nasiru Idris na ciki.

Saidai duk da bayyanar wannan rahoto sama da awanni 48 har yanzu gwamnatin jihar ta Kebbi bata ce uffan ba kan lamarin. Dalilin da yasa wasu ke jin cewa akwai kanshin gaskiya kan lamarin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo yanda aka kama wani mutum Turmi da Tabarya yana làlàtà da matar aure me ciki

Hakanan la’akari da cewa duka Sanatoci 3 na jihar Kebbi a majalisar tarayya ‘yan PDP ne shima na kara rura wannan wutar ta komawar gwamnan jihar PDP.

Hakanan koda a zaben da ya gabata Gwamna Idris yaci zabenne ba da wata tazara me yawa ba inda ya samu kaso 52 cikin 100 na duka kuri’un da aka kada a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *