
Wata kungiyar dake saka ido kan yanda Gwamnati ke gudanar da ayyukanta, NEFGAD ta caccaki Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda kaddamar da wani karamin sashe na titin Legas zuwa Calabar.
Kungiyar ta bakin wakilinta, Mr Akingunola Omoniyi tace yaudara ce kawai ace an kaddamar da kaso 4 cikin 100 na aikin wanda gaba dayansa ne ake bukata.
Kungiyar tace kamata yayi a mayar da hankali wajan kammala aikin bawai wajan tallatashi ba.