Saturday, March 15
Shadow

An yi Gàrkùwà da mutane da yawa a kusa da Barikin Sojoji a Abuja

Rahotanni daga babban birnin Tarayya Abuja na cewa, masu garkuwa da mutane sun sace mutane da yawa a kusa da barikin sojoji ta Abacha Barracks dake Guzape.

Lamarin ya farune da daren ranar Talata.

Lamarin ya farune da misalin karfe 11:31pm kuma ya saka tsoro a zukatan mutane Mazauna Abuja.

Hakan na zuwane biyo bayan garkuwa da mutane data faru a unguwannin Bwari, Kuje, da Gwagwalada wanda cikin wadanda aka yi garkuwar dasu hadda kananan yara da mata.

Hukumar ‘yansandan Birnin na Abuja sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce sun kai dauki wajan da lamarin ya faru kuma sun gano motoci biyu wanda ake tsammanin mutanen ciki ne aka yi garkuwa dasu.

Karanta Wannan  Gwajin ciwon koda

Ciki hadda Hon. Shagala Samuel. ‘Yansandan sunce sun bincike dazukan dake kusa da inda aka yi garkuwa da mutanen amma basu ga wadanda aka sace din ba.

Sannan an sanar da ‘yansandan dake hanyoyin shiga da fita na Abuja su kasance cikin shirin ko ta kwana dan kama wadannan bata gari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *