Monday, December 16
Shadow

An yi hasashen ƴan Najeriya miliyan 33 za su yi fama da yunwa a 2025

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa yunwar da ake fama da ita a Najeriya zai iya tsananta a shekarar 2025, inda aka yi hasashen cewa aƙalla mutum miliyan 33 ne za su iya shiga yunwa a shekarar ta baɗi.

Ƴan Najeriya a yanzu sun kai kusan miliyan 223.8.

A rahoton, wanda Cadre Harmonisé ta yi a ƙarƙashin kulawar gwamnatin tarayya, da haɗin gwiwar shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ne ya bayyana hakan, inda rahoton ya yi hasashen cewa ƴan ƙasar aƙalla miliyan 33.1 ne za su fuskanci yunwa.

Rahoton ya ta’allaƙa hasashen ne kan yanayin taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar da hauhawar farashin kayayyaki da sauyin yanayi da rikce-rikice a wasu yankuna na arewacin ƙasar.

Karanta Wannan  ALLAHU AKBAR: Yau Marigayi Sheik Abubakar Gero Argungu Ke Cika Shekara Guda Cif Da Rasuwa

Rahoton ya ƙara da cewa tsakanin Oktoba zuwa Disamban 2024, kimamin mutum miliyan 25.1 ake hasashen za su yi fama da yunwa, duk da cewa lokaci ne na kakar girbin amfanin gona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *