Me magana da yawun Jam’iyyar APC, Felix Morka ya bayyana cewa, an aika masa barazanar kisa har guda 400 wanda daga ciki guda 200 kai tsaye aka ce za’a kasheshi ko yankashi saboda yayi magana akan Peter Obi.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na AriseTV inda yace an masa kazafin cewa ya yiwa rayuwar Peter Obi Barazana.
Yace shi karya ake masa, babu inda yawa rayuwar Peter Obi Barazana.
Yace tuni aka fara kaiwa wasu daga cikin ‘yan uwansa hari inda yace ya dauki bayanai akan wannan barazana da ake masa inda zai kaiwa hukumar ‘yansanda korafi.
A baya dai, Shima Peter Obi yace ana yiwa rayuwarsa barazana.