
Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama mutum ɗaya bisa zargin kashe tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jama’are Isa Wabi.
A cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma’a, waɗanda ake zargin abokan ɗansa ne kuma sun aikata kisan ne da tsakar daren yau a gidansa da ke Fadaman Mada.
Nan take aka kai shi asbitin Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa bayan rahoto ya ishe ‘yansandan cewa wasu matasa sun caccaka masa wuƙa a wuya.
“Binciken farko-farko ya nuna wasu mutum biyu ne suka aikata kisan waɗanda abokan ɗan Wabi ne ɗan shekara 24 mai suna Abdulgafar Isa Mohammed,” a cewar sanarwar.
Ta ce dakaru sun tarar da ɗaya daga cikin mutanen a sume kuma aka kai shi asibiti, inda daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.
‘Yansanda sun ce sun kama Abdulgafar domin ci gaba da bincike.