
Maganganu na ta yawo cewa, shahararren mawakin Najeriya, Burna Boy ya yaudari wata babbar yarinya da take wuta a birnin Legas me suna Sophia Egbueje inda yayi lalata ita da sunan zai sai mata motar Lamborghini amma bai cika mata alkawari ba.
Yanda aka san labarin shine Sophia ta baiwa kawarta labarin abinda ya farune inda kuma hirar tasu ta watsu a kafafen sadarwa.
A cikin muryar da aka nada, an ji Sophia na bayar da labarin cewa, sun gama rawa da Burna Boya a gidan rawa inda ya kaita gidansa ya kasheta da kalamai ita kuma ta yadda yayi lalata da ita da sunan zai sai mata motar.
Tace daga baya ma kwata-kwata ya daina kiranta.
Tuni dai akai ta mayar da martani kan lamarin inda da yawa suka rika mata dariya da kiranta marar wayau.