
An fara cece-kuce saboda ba’a ga mace ko daya ba a wajan sakawa kasafin kudin shekarar 2025 hannu da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi.
A jiya Juma’a ne dai shugaban kasar ya sakawa kasafin kudin na shekarar 2025 hannu.
Hakan na zuwane yayin da ake ikirarin samar da daidaito ko Adalci tsakanin maza da mata wajan rike mukaman gwamnati da wakiltar jama’a.
Shugaban ya sakawa kudirin dokar hannu ne a fadarsa dake Abuja, kuma bikin ya samu halartar Ministan Kudi, Wale Edun, Shugaban majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio, da takwaransa na Wakilai, Tajudeen Abbas da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Femi Gbajabiamila.
A ciki kuma akwai Nuhu Ribadu wanda shine me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar tsaro da Ministan babban birnin tarayya, Nyesome Wike da sauransu.
Wasu daga cikin matan da aka yi tsammanin gani a wajan taron sakawa kasafin kudin hannu sun hada da ministar masana’antu, Jumoke Oduwole, da karamar Ministar babban birnin tarayya, Mariya Mahmoud, sai karamar ministar kudi, Doris Uzoka-Anite.