
Dan gidan Marigayi shahararren mawakin Najeriya, Fela Kuti Watau Seun Kuti ya bayyana cewa an fi kashye Musulmai a Najeriya fiye da Kirista.
Ya bayyana hakane a matsayin martani ga cece-kucen dake faruwa a Najeriya bayan da kasar Amurka tace ta samu bayanai da suka tabbatar mata cewa ana yiwa Kiristoci Kyisan Kare Dangi a Najeriya.
A Bidiyon Seun da ya watsu sosai yace wannan ikirari ba gaskiya bane.