
Arewa ba ta da hujjar zargiɲ Tinubu na nuna mata wariya -inji Gwamna Uba Sani
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce Arewa ba ta da hujjar zargin Shugaba Bola Tinubu da nuna wariya. Ya bayyana cewa Arewa tana da muhimman mukamai a gwamnati kamar harkar noma da tsaro.
Uba Sani ya kuma ce Jihar Kaduna ta samu ci gaba a fannin noma da zaman lafiya karkashin gwamnatin Tinubu, inda babu rikicin addini ko kabilanci a cikin shekaru biyu da suka gabata. Ayau News ta ruwaito Gwamnan ya bukaci shugabannin Arewa da su daina siyasantar da komai, su mayar da hankali kan aiki da cigaban al’umma.
Me zaku ce?