
A yayin da dambarwar sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio ke ci gaba da bayyana inda take zarginsa da cewa ya nemi yin lalata da ita.
An koma baya a tarihi a lokacin Sanata Godswill Akpabio yana ministan Ma’aikatar harkokin Niger Delta, Tsohuwar shugabar riko ta hukumar raya yankin Niger Delta watau NDDC, Joy Nunieh ta zargeshi da cewa ya nemi yin lalata da ita.
A wancan lokacin har fallaasa mari ta yi inda tace dalili shine ya bata kudi wai ta yadda yayi lalata da ita.
Matar dai itama ta bayyana wannan zargi ne a gidan talabijin na Arise TV inda tace yana tunanin zai iya canja mata tunani da kudi?
Tace itace mace ta farko data taba falla masa mari amma yaki gayawa mutane kuma tana zarginsa da neman yin lalata da ita.
Saidai a wancan lokacin Akpabio yace bata da lafiya ya kamata ta je ta ga likita.