Monday, March 24
Shadow

Ashe ba yau aka fara ba: Yanda wata mata ta taba Fallawa Sanata Godswill Akpabio mari bisa zargin cewa ya bata makudan kudi dan ta amince yayi lalata da ita

A yayin da dambarwar sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio ke ci gaba da bayyana inda take zarginsa da cewa ya nemi yin lalata da ita.

An koma baya a tarihi a lokacin Sanata Godswill Akpabio yana ministan Ma’aikatar harkokin Niger Delta, Tsohuwar shugabar riko ta hukumar raya yankin Niger Delta watau NDDC, Joy Nunieh ta zargeshi da cewa ya nemi yin lalata da ita.

A wancan lokacin har fallaasa mari ta yi inda tace dalili shine ya bata kudi wai ta yadda yayi lalata da ita.

Matar dai itama ta bayyana wannan zargi ne a gidan talabijin na Arise TV inda tace yana tunanin zai iya canja mata tunani da kudi?

Karanta Wannan  Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Murik ta jawo hankalin musulmai da kada su shiga yajin aiki

Tace itace mace ta farko data taba falla masa mari amma yaki gayawa mutane kuma tana zarginsa da neman yin lalata da ita.

Saidai a wancan lokacin Akpabio yace bata da lafiya ya kamata ta je ta ga likita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *