
Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya tabbatar da komawar dansa Abba Abubakar Jam’iyyar APC.
Ya bayyana cewa, komawar dan nasa APC ra’ayinsa ne bashi da hannu a ciki.
Yace a Dimokradiyya ake, baya tursasawa ‘ya’yansa ra’ayin siyasa.
Yace abinda ke gabanshi shine mulkin zalunci da ake a Najeriya da kuma matsin tattalin arzikin da kasarnan ke ciki.