Friday, December 5
Shadow

Atiku ya bukaci a saki Sowore

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi Alla-wadai da kamawa tare da tsare fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore.

Atiku ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido na sufeto janar na ƴansandanƙasar suka yi wa Sowore.

“Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ba ya cikin ka’ida. Dole ne a yi tur da batun,” in ji Atiku.

Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin adalci da kuma kyayyawar shugabanci da ake yi a Nijeriya.

Wasu rahotanni ma na bayyana cewa an lakaɗawa Sowore duka har ma ƙarya masa hannu, inda ake zargin ƴansanda da aikatawa.

Karanta Wannan  Ji yanda matar aure ta mutu bayan da mijinta ya sha maganin karfin Maza yayi jìmà'ì da ita

Wazirin na Adamawa ya ce wannan abin da ƴansanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai bane, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Najeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.

“Don haka muna buƙatar a saki Sowore cikin gaggawa ba tare da ginɗaya wasu sharuɗa ba,” in ji Atiku.

A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami’an ƴansanda domin amsa wasu tambayoyi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *