
Rahotanni daga bangaren Atiku na cewa jiga-jigai sun nemi hada kai da Peter Obi ganin yana da mabiya sosai musamman a kudancin Najeriya.
Rahoton yace an nemi goyon bayan Peter Obi dan ya zama mataimakinsa a shekarar 2027 dan su kwace mulki daga hannun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Rahoton yace bangaren Atiku sun yi Alkawurin yin mulki sau daya inda a shekarar 2031, za’a barwa Peter Obi shi kuma yayi takarar shugaban kasa.
Saidai bangaren Peter Obi sun ki amincewa inda suka ce ai kudu bata kammala wa’adinta na zango biyu ba kamar yanda Buhari yayi.
Dan haka suka ce idan ba Peter Obi bane zai zama ahugaban kasa ba, to basu yadda ba.
Saidai ana ganin har yanzu wannan tattaunawa bata kare ba inda ake tsammanin zata iya cimma gaci.