Dole Tinubu ya dauki mataimaki Kirista ko kuma ya fadi zabe a 2027>>Inji Wata Kungiyar Kirista
Wata kungiya me suna Northern Ethnic Nationality Forum ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu barazanar faduwa zabe muddin bai daiki mataimaki Kirista ba.
Kungiyar ta bakin shugabanta,Dominic Alancha ta jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da cewa, kada ya maimaita kuskuren sake zabar Muslimi a matsayin abokin takararsa a 2027.
Alancha yace dolene Tinubu ya dauki mataimaki Kirista daga daya daga cikin jihohin Plateau, Benue, ko Taraba dan kaucewa tunanin da akewa gwamnatinsa na son mayar da Najeriya kasar Musulmi.
Sun yi gargadin cewa, sakw daukar musulmi a matsayin mataimaki, zai sa 'yan Adawa su yi nasara.







