Sojoji a jihar Taraba sun kubutar da wani jami'in hukumar NDLEA da wasu 5 da aka yi garkuwa dasu.
Lamarin ya farune ranar 27 ga watan Afrilu a kan hanyar dake tsakanin Wukari–Kente a jihar ta Taraba.
Sojojin sun ce wani shugaban matasa me suna Samuek ne ya kira ya sanar da cewa ya ga mota Hulix a daji ba kowa a ciki.
Ko da sojoji suka je gurin motar ba kowa inda daga nan ne suka bazama neman mutanen cikin motar.
An kubutar da su duka, saidai Rahoton yace da kansu ne suka tsere cikin daji bayan 'yan Bindigar sun harbesu da Bindigar farauta.
Sojoji sun gyara musu tayar motarsu data lalace sannan aka rakasu kan hanya suka ci gaba da tafiyarsu.
cikin wata hira da akayi dashi a gidan radio Rahma dake jihar Kano Dr Baffa Bichi ya ce ba wannan ne karon farko da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake tsayawa takara amma yake gaza yin nasara ba.
’’Kwankwaso yayi takarar shugaban kasa a jam’iyar APC bayyi nasara ba yayi a jam’iyar PDP nan ma bayyi nasara ba a shekara ta 2019 da temakon Atiku Abubakar, yayi takara don yayi nasara a jihar Kano amma dashi da Atiku suka fadi ko karamar hukumar sa ta kwankwaso bai kawo ba.
Ya ce a lokacin da Kwankwaso yayi hadaka da Atiku Abubakar bayyia nasara ba ta yaya a yanzu da ya koma sabuwar jam’iya shi kadai zayyi hakan ba zai taba yiwu ba.
Dr Baffa Bichi ya kara da cewa la’akari da bangaranci da son kai na Kwankwaso da kuma kasancewar Atiku Abubakar yana takara a yanzu wannan wata dama ce ga Ja...
Wata kungiyar Matasan Arewa Masu goyon Bayan Bola Tinubu Wadda take da yawan Mabiya miliyan 100 ta yiwa Shugaban ƙasa Bola Tinubu Alƙawarin kawo Masa Miliyoyin kuri'un Matasan Arewa a kakar zaɓe Mai zuwa ta 2027.
Wata ƙungiyar matasa masu rajin goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ake kira City Boy Movement ta sha alwashin tara ƙuri’u fiye da miliyan biyar daga matasa domin tallafawa sake tsayawar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 mai zuwa.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar, Mista Francis Shoga, ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ranar Litinin a Maryland, Ikeja, jihar Lagos, wanda aka shirya domin fayyace manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu ga matasan Najeriya.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar, Mista Francis Shoga, ne ya bayyana haka a yayi...
Kotu ta kori ƙarar da aka kai Buhari da Emefiele kan sauya fasalin takardar Naira
A jiya Litinin ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta kori karar da aka shigar kan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ana neman fansar Naira biliyan 1 kan wahalhalun da tsarin sake fasalin Naira na 2023 ya haifar.
Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya yi watsi da karar bisa hujjar cewa wanda ya shigar da karar bai maida hankali kan shari'ar ba.
Wani lauyan mazaunin Abuja, Uthman Tochukwu SAN ne ya shigar da karar, wanda ya zargi wadanda ake ƙarar da jefa ƴan Najeriya cikin wahala mai tsanani ta hanyar wannan shiri na sake fasalin Naira.
Karar, mai lamba FHC/ABJ/CS/418/2023, ta haɗa da Buhari da babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma tsoho...
Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC, sun kama ƴar bokon nan kuma ƴar kasuwa, Aisha Sulaiman Achimugu.
Lauyan Achimugu, Chikaosolu Ojukwu ne ya shaida wa Nairametrics a wani sako da ya aike a safiyar yau Talata.
Ya ce an kama Achimugu daga saukar ta daga jirgi bayan ta dawo daga London da misalin ƙarfe 5 na asuba.
Tun a baya, lauyan Achimugu ya baiyana wa babbar kotun tarayya a Abuja cewa a yau wacce ya ke karewa za ta kai kan ta ga EFCC a binciken zargin da ake mata na karkatar da wasu kuɗaɗe.
Wani Babban maamin Kirista daga kasar Jamus, Gerhard Ludwig Müller yayi gargadin cewa sabon fafaroman da za'a zaba kada ya zama yana goyon bayan 'yan Luwadi da Madigo.
Ya bayyana cewa duk matsin lambar da za'a masa kada ya goyi bayan wannan kazanta.
Yace Baibul ya koya musu aure tsakanin mace da namiji ne kawai inda ya yi Allah wadai da masu neman halasta auren jinsi.
Daya daga cikin abinda marigayi Fafaroma Francis yayi suna dashi shine neman baiwa 'yan Luwadi da madigo kariya.
Watarana Talakawa Za Su Yi Kukan Rashin Shugaban ƙasa Bola Tinubu A Najeriya, inji fadar shugaban ƙasa
Yan Nigeria "Zaso Ace Bola Tinubu Ya Zarce Ya Zama Shugaban Ƙasa Na Din-din-din, Saboda Duk Ranar Da Bola Tinubu Ya Bar Mulki Sai Talakawan Ƙasar Nan Sun Koka".
Masu karatu me za ku ce?
Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya isa kotu a yau dan ci gaba da shari'arsa.
https://twitter.com/EmekaGift100/status/1917128307637694598?t=uuz52mmUr_1wUALLMm-MVQ&s=19
A wajen kotun kuma magoya bayansa ne suka taru inda suke wakokin yabonsa
Wasu 'yan Arewa da aka tare a jihar Oyo yayin da suka je wucewa ta cikin jihar sun auna arziki inda duka suka tsere.
A baya irin wannan ta taba faruwa a jihar Edo inda aka dake wasu mafarauta wanda aka zarga da cewa masu garkuwa da mutanene har sai da suka daina motsi sannan aka cinna musu wuta.
Saidai a wannan Karin basu tsaya ba.
https://twitter.com/ChuksEricE/status/1916569234085228586?t=Gi7A32-KGIxup14WqmVJZg&s=19
An ji mutanen dake magana a cikin Bidiyon suna kiran mutanen da 'yan Bòkò Hàràm duk da yake cewa babu wata hujja data tabbatar da hakan.