Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Hotunan masanin Kimiyya da babban soja da kasar Israyla ta kàshè a harin da ta kaiwa Ìràn

Kalli Hotunan masanin Kimiyya da babban soja da kasar Israyla ta kàshè a harin da ta kaiwa Ìràn

Duk Labarai
Kasar Israyla ta sanar da cewa gurare a kalla 12 ne ta kaiwa hari a cikin kasar Ìràn ciki hadda tashar makamashin kare danginta. A harin an kashe masanin Kimiyya, Martyr Fakhrizadeh Da kuma shugaban rundunar sojojin ta Revolutionary Guard wanda aka fi sani da IRCG me suna Janar Hossein Sulaimani. Kasar Iran tace hadakatar kasashen Israyla da Amurka ne suka kai mata wannan hari kuma zata mayar da martani me karfi. Kasar Iran tace ba zata bari wannan ya tafi a banza ba
Bamu da hannu a harin da kasar Israyla ta kawo muku, kada ku tabamu>>Amurka ta gayawa Ìràn

Bamu da hannu a harin da kasar Israyla ta kawo muku, kada ku tabamu>>Amurka ta gayawa Ìràn

Duk Labarai
Kasar Amurka ta gayawa Iran cewa, kasar Israyla bata nemi shawarar ta ba kamin afka mata da yaki. Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar. Amurka tace bata taimaki kasar Israyla ba ko bayar da hadin kai wajan harin da ta kaiwa kasar ta Iran ba. Yace dan haka Iran kada ta taba sojojin kasar Amurka ko gine-ginen ta dake yankin na gabaa ta tsakiya. Yace kasar Israela tace ta dauki wannan mataki ne dan kare kanta. Yace aikinsu shine sh baiwa sojojinsu kariya. Kasar Israyla tace gurare 12 ne ta kaiwa hari a kasar Iran ciki hadda tashar Nukiliyar ta. Kasar Amurka ta baiwa mutanen ta musamman na ofishin jakadancin ta umarnin su yi ta kansu, ko su shiga maboya me bayar da kariya ga bom dan a ko da yaushe kasar Iran zata iya k...
Da Duminsa: A karshe dai Kasar Israyla ta Afkawa Ìràn da yàkì, ta kaiwa tashar sarrafa Urànìyùm ta kasar hàrì inda kuma ta kàshè babban janar din sojan Ìràn

Da Duminsa: A karshe dai Kasar Israyla ta Afkawa Ìràn da yàkì, ta kaiwa tashar sarrafa Urànìyùm ta kasar hàrì inda kuma ta kàshè babban janar din sojan Ìràn

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Rahotanni dake fitowa daga gabas ta tsakiya na cewa kasar Israyla ta kaiwa tashar Nùkiliya ta kasar Ìràn hari. Rahoton yace harin ya kashe babban janar me kula da rundunar da ake kira Revolutionary Guard ko IRGC na kasar Iran me suna Janar Hossein Salami. Kafofin yada labarai na kasar Iran din sun tabbatar da hakan. Tashar talabijin ta kasar Iran ta nuna wasu gine-gine a kasar na ci da wuta bayan harin. Kasar Israyla tace zata ci gaba da kaiwa Iran harin har sai ta nakasa s...
Ji Cikakken Bayani kan hadarin jirgin saman Indiya inda mutane sama da 200 suka mùtù, an bayyana kudin diyyar da kamfanin jirgin zai biya iyalan màmàtàn

Ji Cikakken Bayani kan hadarin jirgin saman Indiya inda mutane sama da 200 suka mùtù, an bayyana kudin diyyar da kamfanin jirgin zai biya iyalan màmàtàn

Duk Labarai
Wani jirgin sama mallakin kamfanin sufuri na Air Indiya ya yi hatsari inda ya faɗa kan wata unguwa da ke birnin Ahmedabad a yammacin ƙasar Indiya. Shugaban kamfanin lura da sufurin jiragen sama na Indiya ya ce akwai fasinjoji da ma'aikata 242 a cikin jirgin. Bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta ya nuna baƙin hayaƙi ya turnuƙe bayan rikitowar jirgin. Babu tabbacin adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata sanadiyyar hatsarin. Jirgin na kan hanyarsa ne daga Indiya zuwa Birtaniya. Ma'aikatan kashe gobara da masu bayar da agajin gaggawa sun garzaya wurin da lamarin ya faru. Akwai yiwuwar dukkanin fasinjojin jirgin Indiya da ya yi hatsari sun mutu Kamfanin dillancin labaru na AP ya ambato shugaban ƴansanda na birnin Ahmedabad na cewa akwai yiwuwar babu wanda ya ts...
Ya kamata a dawo da tallafin aikin hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume

Ya kamata a dawo da tallafin aikin hajji ga maniyyatan Najeriya – Ndume

Duk Labarai
Jagoran ƴan kwamitin majalisar dattijan Najeriya kan harkokin ƙasashen waje a lokacin aikin hajjin 2025, Sanata Ali Ndume ya buƙaci da a mayar da tsarin bayar da tallafi kan batun aikin hajji a ƙasar domin rage tsadar kujera ga maniyyata. Ndume ya fadi haka ne a tattaunawarsa da BBC jim kadan bayan kammala aikin hajjin 2025 a ƙasar Saudiyya. Sanatan wanda ya nuna gamsuwa kan tsarin da aka samar ga mahajjatan Najeriya a Saudiyya ya ce "dama gwamnatin da ta shuɗe ita ce ta cire tallafin da ake bayarwa kan aikin hajji, saboda haka ya kamata a dawo da bayar da tallafi saboda aikin hajjin ya yi tsada." Mahajjatan Najeriya a 2025 sun biya kuɗin kujera ne tsakanin naira miliyan 8.3 zuwa miliyan 8.8 dangane da ɓangaren ƙasar da suke zama. Hakan ya ɗara abin da maniyyatan Najeriya suka ...
Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa cikin matsala – Tinubu

Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa cikin matsala – Tinubu

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana farin ciki da halin rikici da jam'iyyun adawa da dama na ƙasar ke ciki. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin jawabin da ya yi na ranar tunawa da dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, yau Alhamis. "Ina jin daɗin ganin jam'iyyun adawa a tagayyare," kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya. Tinubu ya ce "ba zan ce ina so na ga kun gyaru ba, ina ma jin dadin ganin ku a haka. Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar ke ci gaba da karɓar ƴan siyasa masu sauya sheƙa daga jam'iyyun adawa zuwa cikinta. Tinubu ya ce jam'iyyar APC ba za ta hana kowa shiga cikinta ba domin yin hakan tauye hakkin al'umma ne.
Kungiyar dake saka ido kan makamin kare dangi ta Duniya tace kasar Ìràn ta munafurceta ta hanyar kin bayyana mata shirin da take na mallakar makamin

Kungiyar dake saka ido kan makamin kare dangi ta Duniya tace kasar Ìràn ta munafurceta ta hanyar kin bayyana mata shirin da take na mallakar makamin

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sanya ido kan mnakaman nukiliya ta yanke hukuncin cewa Iran ta karya ƙa'ida da aka shimfiɗa kan makaman Nukuliya. Bayan an kaɗa ƙuri'ar makamai a Vienna, hukumar ta kuma nemi Iran ta yi bayanin yadda aka gano kayan haɗa makaman nukiliya a wasu yankuna da Tehran ba ta bayyana ba. Daukar sabon matakin zai iya kaiwa ga sabbin takunkuman da aka janyewa ƙasar shekaru 10 da suka gabata. Da Iran take mayar da martani ta ce, sakamakon hukumar cike...
APC ta zargi Gwamnatin Kano da ciyo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasar waje tare da neman bahasin yadda aka yi da kuɗaɗen

APC ta zargi Gwamnatin Kano da ciyo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasar waje tare da neman bahasin yadda aka yi da kuɗaɗen

Duk Labarai
APC ta zargi Gwamnatin Kano da ciyo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasar waje tare da neman bahasin yadda aka yi da kuɗaɗen Wata ƙungiya a cikin jam’iyyar APC a jihar Kano mai suna APC Patriotic Volunteers ta zargi gwamnatin jihar da karɓar bashi daga ƙasashen waje har Dala Miliyan 6.6 ba tare da bayyana inda kuɗaɗen suka tafi ba. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Usman Alhaji ne ya yi wannan zargi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano a yau Laraba. Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa taron manema labaran an shirya shi ne domin nazarin ayyukan gwamnatin jam’iyyar NNPP a Kano cikin shekaru biyun da ta yi a kan mulki. A cewar Alhaji Usman, ƙungiyar na da hujjoji daga Ofishin Kula da Lamuran Bashi na Ƙasa (DMO) da ke nuna cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta karɓi bas...
Yarbawan Arewa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin Kuri’u Miliyan 10 a zaben 2027

Yarbawan Arewa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin Kuri’u Miliyan 10 a zaben 2027

Duk Labarai
Kungiyar yarbawa magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me suna (NOYAT) sun yiwa shugaban kasar Alkawarin samar masa da kuri'u Miliyan 10. Kungiyar a shekara 2022 ta shirya taro na musaman kan goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Kaduna wanda ya samu halartar manyan mutane ciki hadda malaman addini. A sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Laraba, ta sanar da cewa, tana jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda nada Yazeed Shehu Danfulani shugaban hukumar inshora ta manoma ta kasa, (NAIC). Kungiyar a sanarwar wadda kakakinta, Mr. Seun Ogunyinka ya ftar tace nadin ya karfafa matasa sannan kuma 'yan Najeriya da dama sun ji dadi inda suka bayyana Danfulani a matsayin gwarzo wanda aka sanshi da aiki Tukuru.