Ji Dalilin da yasa Kasar Saudiyya ta hana Sheikh Dr. Ahmad Gumi yin aikin Hajjin bana, kamar yanda yayi karin bayani
Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun hana babban malamin addinnin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin hajjin bana.
Sheikh Gumi wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa gwamnatin Saudiyya bayan ta ba shi bizar shiga ƙasar domin aikin Hajji amma kuma sai ba a ba shi damar shiga Madina domin fara aikin ibada ba.
"Bisa waɗansu dalilai saboda ra'ayi na kan siyasar duniya, hukumomi a Saudiyya ba sa son kasancewata a Hajji duk da sun ba ni biza," in ji Sheikh Gumi kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya ƙara da cewa "Ina godiya ga hukumomi a Najeriya waɗanda suka sha alwashin tuntuɓar hukumomin Saudiyya a kan wannan lamarin."
Bayanan da BBC ta tattaro sun nuna cewa Sheikh Ahmad Abubakar Gumi na cikin tawagar malaman da hukumar aikin hajjin...








