Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Duk Labarai
Hamshakin me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa, nan da shekaru 20, watau 2045 zai Rabar da gaba dayan kudinsa. Bill Gates ya bayyana hakane a shafin Gidauniyarsa ta Bill and Melinda Gates wadda suka kafa a shekarar 2000. Daga baya Wallen Buffet ya shiga tafiyar. Ya bayyana hakane yayin bikin cikar gidauniyar shekaru 25 da kafuwa. Hakanan a shekaru 25, Bill Gates ya bayar da Tallafin da ya kai na dalar Amurka Biliyan 100 kyauta. Yace nan da shekaru 20 din zai nunka yawan kudin da yake bayarwa tallafi har sai kudin sa sun kare gaba daya, bai bayyana cewa zai barwa 'ya'yansa ko sisi ba. Bill Gates wanda shine me kamfanin Microsoft yace zaftare tallafin da kasashe masu kudi suka yi wanda a baya suke baiwa kasashe matalauta abin damuwa ne. Yace baya so idan ya mutu a ri...
Nifa ba da son raina na dawo Najeriya ba, garkuwa dani aka yi>>Inji Nnamdi Kanu

Nifa ba da son raina na dawo Najeriya ba, garkuwa dani aka yi>>Inji Nnamdi Kanu

Duk Labarai
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa ba da son ransa ya dawo Najeriya, garkuwa dashi aka yi. Ya bayyana hakane a yayin zaman kotu dake sauraren kararsa. Yace kuma shi ya kafa kungiyar ESN ne dan su baiwa iyayensu dake shiga daji kariya ba dan su kaiwa kowa hari ba. Da aka tambayeshi game da hare-haren da aka kai kan jami'an tsaro da sauran hukumomin Gwamnati, Nnamdi Kanu yace bai san da wannan ba dan shi baya tayar da Fitina.
Bidiyo: Shugaba Tinubu ya isa jihar Anambra

Bidiyo: Shugaba Tinubu ya isa jihar Anambra

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa jihar Anambra inda yake ziyarar aiki a yau, Alhamis. Shugaban iya isa filin sauka da tashin jiragen sama na Chinua Achebe dake jihar inda ya samu tarbar gwamnan jihar, Charles Soludo da 'yan majalisar jihar da sauran dattawan jihar. Shugaba Tinubu kuma ya samu ya tsaya an masa taken Najeriya inda sojoji suka yi harbi sama dan girmamashi. Bayannan kuma, Shugaba Tinubu ya shiga motar da aka tanada dan shi tare da Gwamnan jihar inda zai zarce dan fara kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta gudanar.
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Duk Labarai
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da Honorable Salisu Yusuf Majigiri na mazaɓar Mashi/Dutsi, Honorable Aliyu Iliyasu na mazaɓar Batsari/Safana/Danmusa, Honorable Abdullahi Balarabe Dabai na mazaɓar Bakori/Danja. Dukkan su sun bayyana rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a matsayin dalilin sauya shekar ta su.
Akpabio ya kai Sanata Natasha Akpoti kara kotu kan takardar Hakuri da shagube data yi masa, Yace yana son Kotu ta sa Natasha ta goge Wasikar a shafinta na sada zumunta sannan ta bashi Hakuri

Akpabio ya kai Sanata Natasha Akpoti kara kotu kan takardar Hakuri da shagube data yi masa, Yace yana son Kotu ta sa Natasha ta goge Wasikar a shafinta na sada zumunta sannan ta bashi Hakuri

Duk Labarai
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu, yana zargin ta da wallafa kalaman ɓatanci a cikin wata wasikar bada haƙuri da aka danganta da ita — Wasikar da ke ɗauke da wata magana mai cin mutunci da ke cewa “ta yi kuskuren tunanin cewa kujerarta a Majalisa ta samu ta hanyar zaɓe, ba ta hanyar jima’i ba.” Rahotanni sun bayyana cewa wannan ƙara ta samo asali ne daga wata wallafa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da Sanata Natasha, inda ta nemi gafara daga Shugaban Majalisar bisa wasu maganganu da ake cewa ta furta a baya. A cikin wannan wasikar, an ambaci cewa ta “yi kuskuren ɗauka cewa ta samu kujera ne ta hanyar sahihin zaɓe.” Lauyoyin Akpabio sun ce wannan magana ta wallafa ra’ayi mai matuƙar cin mutunci da b...
Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye. Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba. Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin. Ambasada Nuhu ya ce "hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al'umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma", in ji shi. "...
An sami rashin fahimta tsakanin ƴan majalisa da ministan tsaron Najeriya kan tsaro

An sami rashin fahimta tsakanin ƴan majalisa da ministan tsaron Najeriya kan tsaro

Duk Labarai
Ministan tsaron Najeriya, Mohamamd Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba, da majalsair dattawwan ƙasar ta nemi a yi ba. Haka kuma ya musanta zargin da majalisar wakilan ƙasar ta yi na cewar ƴan bindigar na amfani da makaman da suka fi na jam'an tsaron ƙasar. A ranar Talata ne dai majalisar dattawan Najeriya suka buƙaci da a shirya wani taro kan harkokin tsaro, don samar da hanyoyin magance matsalar. Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na ministoci da ya gudana a jihar Laraba ministan tsaron na Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya ce sakae dabarun yaƙi da mastaalr tsaro ya kamata a yi ba wai taro ba a halin da ake ciki a ƙasar. "Idan ka yi taron ƙasa kan tsaro, mutane za su zo, su fadi abin da suke so, mu ...
Mayar da Najeriya tsarin Jam’iyya daya na da hadari>>Goodluck Jonathan

Mayar da Najeriya tsarin Jam’iyya daya na da hadari>>Goodluck Jonathan

Duk Labarai
Bayan tsawon lokaci ba a ji ta bakinsa ba dangane da faruwar al'amuran siyasa, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ɓara inda ya yi gargaɗin cewa "abu ne mai haɗari ɗora Najeriya a kan turbar jam'iyya guda ɗaya". Ba kasafai dai ake jin bakin Goodluck Jonathan ba a al'amura kasancewarsa mutum mai kawaici da rashin son yawan magana. To sai dai a ranar Larabar nan, tsohon shugaban na Najeriya yayin wata lacca da aka shirya a Abuja domin tuna wa da marigayi Edwin Clerk, dattijo ɗan ƙabilar Ijaw wanda ya rasu yana da shekara 97, Jonathan ya ja hankalin gwamnati da jam'iyya mai mulki ta APC da ake zargi da mayar da ƙasar ƙarƙashin tsarin jam'iyya guda. Kalaman Goodluck Jonathan Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ce duk wnai yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam'i...