Da Yardar Allah Shekarar 2025 Za Ta Kasance Shekarar Cika Alkawura Da Burikanmu, Sakon Shugaba Tinubu Ga ‘Yan Nijeriya
SAKON SHIGA SABUWAR SHEKARA ZUWA GA 'YAN NIJERIYA
Yan uwana ƴan Nigeria,
A yayin da muka shiga 2025, ina yi wa kowa fatan alheri.
Ina fatan mun shiga shekarar da ƙafar-dama, ƙunshe da farinciki, wadata nasara, da lafiya mai ɗorewa.
Wannan sabuwar shekara da muka shiga, cike take da fatan samun ingantattun kwanaki a cikinta, kuma da yardar Allah, shekarar 2025 za ta kasance shekarar cika alkawura, da burikanmu na bai ɗaya.
Duk da cewa shekarar 2024 ta kasance ɗauke da ƙalubale mai tarin yawa ga ƙasarmu da ƴaƴanta, ina da ƙwarin gwiwar cewa sabuwar shekara za ta zo mana da ƙafar -dama.
Ƴar manuniya ta nuna cewa, juma'ar tattalin arzikin mu ta fara yin kyau tun daga larabarta ga al'ummarmu, farashin man fetur ya fara sauka sannu a hankali, mun sami rara a cinikayyar ƙasa da ...








