
Tsohon Ministan sufuri kuma Gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa, irin ukubar da ‘yan Najeriya ke sha a hannun Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yasa suna rokon tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya dawo kan mulki.
Amaechi ya bayyana hakane yayin ganawa da manema labarai a Abuja inda yace Najeriya ta yi lalacewar da ko da an canja gwamnati ba lallai ta dawo daidai ba
Yace tsadar rayuwa ta yi yawa, mutane basa iya sayen abinci, komai ya lalace.
Amaechi yace ya bar jam’iyyar APC zuwa ADC inda yace ya dade da daina halartar duk wani taron jam’iyyar inda yace ba zai yiyu ya ci gaba da zama a tsakiyar barayi ba.
Yace a lokaci na karshe da APC ta gayyaceshi ya gargadesu kada su sake gayyatarsa.
Amaechi yace gyaran Najeriya sai an tashi tsaye.