
Babban Fasto Chukwuemeka Odumeje wanda yayi kaurin suna wajan jawo cece-kuce, yace ba Allah ne ya zabi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban Najeriya ba.
Yace shugaba Tinubu da karfin tsiya ya kwaci mulkin.
Ya bayyana hakane a wani faifan Bidiyon da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Ya musanta abinda mafi yawan addinai suka aminta dashi na cewa duk wanda ka ga ya zama shugaba to zabin Allah ne, yace game da Tinubu abin ba haka yake ba.