Wednesday, January 15
Shadow

Ba faɗuwa na yi ba, na rusuna ne don girmama dimokuraɗiyya – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya mayar da martani kan faduwar da ya yi lokacin bikin ranar dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yunin 2024.

Bidiyon faduwar shugaban ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ya nuna Tinubu a lokacin da yake yunkurin shiga motar faretin a dandalin Eagle Square da ke Abuja inda ya rasa wani mataki wajen hawar motar ya faɗi.

Tinubu mai shekaru 72, ya ce dimokraɗiyya ta cancanci faduwa.

Da yake magana game da abin da ya faru a ranar Laraba, shugaban ya yi dariya da cewa “na rusuna ne don girmama dimokraɗiyya” a salon Yarbawa.

Shugaba Tinubu ya kuma yi amfani da taron liyafar cin abincin na bikin dimokraɗiyya wajen kira ga hadin kan Nijeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ko siyasa ba.

Karanta Wannan  Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu

Ya kuma jaddada cewa hadin kan Najeriya ba abu ne da za a iya yin cinikinsa ba.

Bayan afkuwar lamarin, an samu martani da dama daga ‘yan Najeriya daban-daban ciki har da ‘yan adawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *