
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ba neman izinin komawa SDP ya je yi wajan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.
Yace ya jene ya sanar dashi a matsayinsa na uban gidansa a Siyasa.
Tsohon Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace wannan bayani ya dole yayishi saboda yanda ake ta samun rahotanni wanda ba daidai ba daga gidajen jaridu.
Bayan komawar El-Rufai SDP kuma yace da sanin tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari yayi hakan, Tsohon shugaban kasar ya fito yace har yanzu yana Jam’iyyar APC saboda ta bashi dama ya zama shugaban kasa har sau 2.