Sunday, August 9
Shadow

Ba neman izinin Komawa SDP na je yi wajan Buhari ba, najene in sanar dashi a matsayinsa na Uban gidana>>El-Rufai

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ba neman izinin komawa SDP ya je yi wajan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.

Yace ya jene ya sanar dashi a matsayinsa na uban gidansa a Siyasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda yace wannan bayani ya dole yayishi saboda yanda ake ta samun rahotanni wanda ba daidai ba daga gidajen jaridu.

Bayan komawar El-Rufai SDP kuma yace da sanin tsohon shugaban kasar, Muhammadu Buhari yayi hakan, Tsohon shugaban kasar ya fito yace har yanzu yana Jam’iyyar APC saboda ta bashi dama ya zama shugaban kasa har sau 2.

Karanta Wannan  Gwanin Ban Tausai: Ji yanda kananan 'yan matan da aka yi gàrkùwà dasu aka sakosu suka koma yin karuwanci saboda 'yan Bìndìgàr sun saba musu da làlàtà

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *