
Tsohon sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya bayyana cewa ba sai tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya goyi bayan dan takara ba kamij dan takar yayi nasara akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba a shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a hirar da jaridar Punchng ta yi dashi inda yace suna zuwa gurin Buhari ne a matsayinsa na babba dan sanar dashi abinda zasu yi ya saka musu Albarka.
Yace amma basa bukatar tsohon shugaban kasar ma ya shiga tafiyarsu dan suna da hankali da wayau sun san yanda zasu gudanar da al’amuransu.
Babachir yace Gwamnatin Tinubu bata son talakawa ne shiyasa take kokarin ganin ta sakasu a wahalar da zata kai su ga halaka.
Yace su kuma abinda suka fito dan karewa kenan talakawa da masu rauni.