
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Bidiyon da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga jirgin samansu yana sauka da tashi a tsakanin wasu masu rike da makamai.
An yi zargin cewa jirgin ya je kaiwa ‘yan Bindiga kayan abinci da sauran kayan aiki ne.
Saidai a sanarwar da ta fitar ta shafinta na sada zumunta, Hukumar ‘yansandan tace ba ‘yan Bindiga bane aka gani a cikin Bidiyon ba. ‘Yansanda ne dake aikin samar da tsaro a dajin Obajana na jihar Kogi.
Hukumar tace a daina dogaro da bayanan da basu fito daga bakin hukumomin tsaro ba dan gujema labarin karya.