
Malamin Kirista, Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa Mulkin musulmi da Musulmi da ake yi a Najeriya ya isa zama cin zarafi na karshe ga Kiristocin kasarnan.
Yace dolene Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauke Kashim Shettima ya dauki Kirista a matsayin mataimaki.
Yace ba zai bari abubuwa su ci gaba da zama a haka ba dan kuwa nan gaba jikokinshi zasu iya komawa musulmai kuma ba zai so haka ba.